Kamfanin dillancin labaran kasar Iran (IRNA) ya bayyana cewar Ayatullah Jannati ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar inda yace: A lokuta da dama al'ummar Iran sun tabbatar wa da duniya sanin ya kamatansu ta hanyar fitowa kwansu da kwarkwatarsu yayin gudanar da zabe, don haka a wannan Juma'ar ma za su sake fitowa don sauke wannan nauyi da ke wuyansu.
A bangare guda kuma shugaban majalisar kwararrun ya kirayi 'yan takaran zaben shugaban kasar da su ba da himma wajen magance matsalolin da al'umma suke fuskanta da kuma gudanar da tsarin tattalin arzikin dogaro da kai da Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar.
A ranar Juma'ar nan mai zuwa, 19 ga watan Mayu ne za a gudanar da zaben shugaban kasar na Iran karo na 12 tsakanin 'yan takara guda hudu, bayan da biyu daga cikin shida na farkon, wato magajin garin Tehran Muhammad Baqir Qalibaf da kuma mataimakin shugaban kasa Ishaq Jehangiri sun janye takarar na su da goya wa biyu daga cikin 'yan takaran wato Sayyid Ibrahim Ra'isi da kuma shugaba mai ci Hasan Ruhani baya.