A cikin wasu sakonni mabambanta da suka fitar, hukumar ta FIFA da kuma kungiyar Manchester United din sun bayyana alhini da kuma ta'aziyyarsu ga 'yan uwa da iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su a ranar Alhamis din da ta gabata.
Shi ma a nasa bangaren, shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ta bakin kakakinsa Garba Shehu, ya ce ya kadu kwarai da jin labarin abin da ya faru wanda ya janyo asarar rayuka da dama. Don haka shugaban ya ce yana isar da sakon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma gwamnati da jama'ar jihar Cross River, haka zalika da masoya kwallon kafa a duk fadin Nijeria.
Wannan lamari dai ya faru ne ranar Alhamis din da ta gabata da daddare a lokacin da jama'a suka taru makil a wani gidan kallon talabijin a birnin na Calabar don kallon wasan kwallon kafa na Europa tsakanin kungiyar Manchester United da Anderletch ta kasar Belgium inda wani babban layin wutar lantarkin ya katse da kuma fadowa kan jama'a inda aka ce alal akalla mutane 30 sun mutu.288