9 Afirilu 2017 - 12:17
Jamus ta dawo da dan IS Najeriya

Jamus ta dawo da wani dan ISIS Najeriya da ta ce yana da matukar hatsari ga hukumomin kasar, sai dai rahotani sun ce mutumin da ba a bayyana sunansa ba, haifafan dan kasar ne ba Najeriya ba.

Matashi da aka ce shekarun 22, tare aka tsare su da wani dan Algria a watan Fabairun da ya gabata kan zargin suna kimtsa kai hari kasar.

Jamus dai ta haramtawa Mutumin shiga kasarta har abada, tare da ci gaba da daukan matakan kare kasarta daga ‘yan ta’adda.