A karshen ziyarar aikin da ya kai kasar Yamen a jiya Talata: Babban daraktan kungiyar bada agajin gaggawa ta kasa da kasa Red Cross a yankin gabas ta tsakiya Robert Mardini ya bayyana cewa: A daidai lokacin da rumbun tsimin abincin kasar Yamen ke daf da karewa nan da watanni biyu zuwa hudu, a gefe guda kuma matsalar fari tana ci gaba da kunno kai a kasar lamarin da zai wurga rayuwar al'umma cikin mawuyancin hali a kasar.
Robert Mardini ya kara jaddada damuwarsa kan yadda kasar Saudiyya da kawayenta suka yi kawanya wa kasar Yamen tare da hana shigar da kayayyakin abinci da na bukatu ga al'umma da suke cikin halin kaka-ni ka yi musamman al'ummar garin Bandar-Jadid da ke yammacin kasar. 288