11 Faburairu 2017 - 15:24
MENENE WANNAN  AL’AMARIN DA ALLAH SUBHANAHU WA TA’ALA YACE “ATA AMRULLAHI FALA TASTA’AJILUH” ? na 2

JAWABIN MAULANA SHEIKH HAMZAH MUHAMMAD LAWAL NA NISFUSH SHA’ABAN 2016 YUSUF SULAIMAN NE YA RUBUTU MAKU

…..cigaba.
Akwai wata riwaya da nake so na kawo tana da dangantaka da abinda muke bahasi akai.Al-Allamah Tabataba’I yana cewa a cikin littafin Al-Gaiba na Nu’umani daga AbdurRahaman Ibn Kabir daga Baban Abdullah (Imam Sadiq )yana cewa dangane da fadin Allah:
“ATA AMRULLAH FALA TASTA’AJILUHU”
Ma’ana; “Al’amarin Allah ya zo saboda haka kada ku gaggauta shi” .Sai As-Sadiq yace shine al’amarin mu al’amarin Allah Azza wa Jal (na bayyanar Hujjah (as) ),saboda haka ka da a gaggauto da zuwan shi din.Allah zai taimake shi in ya zo da rundinoni uku;da Mala’iku da Mu’uminai da kayan aiki (wato ababen hawa(wato ramzi ).
Fitar shi zata zama kaman fitar Manzon Allah (sawa)(wato fita yakin shi).To sai Assadiq yace wannan shine fadin Allah Ta’ala:“Kaman yanda Ubangijinka Ya fitar da kai daga gidan ka da gaskiya”,kaman yanda ya faru a Manzon Allah haka zai dabbaku a lokacin fitar Al-Hujja,wato Allah zai fitar dashi daga gidan shi da gaskiya.To me ake nufi da wannan “da gaskiya”?Ana nufin da nasara wato zai INTISARI akan kowa da kome.
Sannan Al-Allamah Tabataba’I ya sake cewa sai nace:kuma Ash-Shaikhul Mufid ya rawaito shi a littafin Al-Gaiba din shi daga AbdurRahman daga gare shi As-Sadiq (as)cewa manufar wannan ayan da manufar wannan riwayar daga A’immah shine bayyanar Imam Mahdi (as) kaman yadda Al-Imam (as) ya sarraha kiri-kiri a wasu riwayoyi daban banda wannan-wato akwai riwayoyi masu yawa-Sai Allamah yace wannan yana daga cikin JARYIN Alkur’ani ko badinin ayan,wato ayan a zahirin ta ga ma’anar ta,sannan a sauran dabaqoqin ta ga ma’anar ta.
Sannan ban da haka,akwai wurare daban daban a cikin Al-Kur’ani din wa’yanda ba ina so in kawo duka bane duk da yake ga su,in da akayi ishara da cewa zuwan Manzon Allah (sawa)shine karshen lokaci.In muka ajiye littafin Allamah Tabataba’I muka zo dayan littafin Al-Gaiba din kuma na As-Shaikhud Dusi-akwai su da yawa-shi kuma a wani bangare kadan,kaman bangaren shekarun shi(as) wato shekarun da zai yi a doron kasa in ya zo(Al-Hujjah in ya zo).
Akwai riwayoyi masu yawan gaske wadanda dole sai malamai ne suke iya hada su,kuma anan din yayi kokarin ya hada su.Cewa miqdarin rayuwar shi da shekarun shi Al-Hujjah (as).Yana cewa:
“Hakika mun yi bayani a da a cikin littafin da hadisai ingantattu akan cewa haihuwan Sahibuz Zaman ta kasance a shekara ta 256 –a wurin shi  shi,ko 255 a wurin wasun shi-Kuma cewa mahaifin shi ya rasu ko an kashe shi a shekara ta 260.Kenan a wannan riwayar shekaran shi Al-Imamul Hujjah hudu mahaifin shi ya rasu,a wasu riwayoyi shekarun sa biyar.Daga nan zuwa karshen duniya shekara nawa zai yi,wato daga wannan shekara hudu ko biyar shekara nawa zai yi?kuma wannan shine mahallin shubha da ishkal na mutanen yau da kullum,cewa daga lokacin ko 255 ko 256 zuwa lokacin da Allah Subhanahu wa Ta’ala Ya so ya rayu zai yi shekara nawa?
To a lokacin shekaran shi hudu (a riwayar shi ,to kenan shekarun shi daga lokacin zuwa lokacin da zai bayyana ba ma lokacin da zai bar duniya ba tukuna.Daga lokacin zuwa lokacin da zai bayyana shekarun shi za su zama abin da lissafi ya bayar.Wato a shekarar da ya bayyana aka gani sai a kara shekara nawa?Sai a kirgo daga wancan lokacin sai a ce yanzu shekaran shi kaza.Daga nan kuma sai a cigaba da kirga wa har zuwa lokacin da shi kuma zai bar duniya.
Yace abin da lissafi ya bayar shine zai zama shekarun shi.Wato in kana so ka san daga lokacin zuwa yanzu misali,shekarar shi nawa zaka iya sani.Sannan lokacin da ya bayyana kuma shekaran shi nawa.Wato daga lokacin da aka haife shi shekarar shi nawa shima zaka iya sani kuma yana hannun ka saboda lissafi ne.Zai zama abin da lissafi ya bayar.Kuma wannan bai yin karo da sauran riwayoyi da aka riwaito wa’yanda suke magana akan gwargwadon shekarun shi da suka bambamta a lafazi.Kaman irin riwayoyin da-ya kamata mutane su san riwayoyi daban daban saboda mutane suna fadin maganganu kala-kala akan Imam Mahdi (as) amma da kai,basu san cewa ba al’amari ne wanda yake na shashi fadi ba haka nan,ijtihad ne,kuma fagen malamai-kaman riwayoyi wa’yanda suka zo suna masu bayanin shekarun shi Al-Hujjah (AS) da lafuzza daban daban.Kaman abin da aka rawaito daga Abu Ja’afar Al-Baqir (as) yana cewa :
“LAISA SAHIBU HAZAL AMR MAN JAZAL ARBA’IN”
Ma’ana:Ma’abucin wannan al’amarin –amruna ko?ATA AMRULLAH- ba shi bane wanda ya wuce shekara arba’in.Wato lokacin da zai bayyana ba yanda za a yi ya wuce shekara arba’in.Ya zaka hada riwayoyin?Ma’abucin wannan al’amarin ba shi bane wanda ya wuce arba’in.Da irin wadannan labaran na daga riwayoyi,da kuma sauran riwayoyi irin wa’yanda suka gangaro da lafuzza masu sassabawa da kuma ma’anoni daban daban masu sassabawa juna.
To yaya zaka yi TAUSIQIN cewa shekarun shi  a lokacin da zai bayyana shine abinda lissafi zai bayar?Da kuma irin wadannan riwayoyin?A nan ne ake bukatar ka saurara,ba a bukatar karambani,sannan ka ji ra’ayoyi daban daban na malamai.Ka da ka dinga daukan riwaya kana naqalto wa mutane,kana gaya masu abubuwan da kake tsammani ka gane alhali baka gane ka.288
Akwai cigaba insha Allah.