Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Sheikh Naim Qassem, babban sakataren Hizbullah ta Lebanon, da yammacin yau Talata a cikin jawabinsa a bikin buɗe cibiyar kiyayewa kula da yaɗa gadon shahidi Sayyid Hassan Nasrallah ya ɗauki kiyaye wannan taska da Shugaban Gwagwarmaya ya bari mai daraja a matsayin wajibi mai muhimmanci.
Babban Sakataren Hizbullah ya nanata cewa: ƙarfafa ababen more rayuwa na fagen gwagwarmaya na shekaru 23 da tsara taswirar hanyar daukaka, 'yanci da farin ciki da shahidi maɗaukaki Sayyid Hassan Nasrallah ya yi, sun bar gado na dabarun da ba za a manta ba ga ƙarnuka masu zuwa.
Ya ƙara da cewa: kiyaye wannan taska mai daraja da rubuta manyan tunaninsa na nazarinsa, al'adu, siyasa da aiki a cikin tsari da aka tattara da kuma yadawa, wajibi ne mai muhimmanci ga fagen gwagwarmaya.
Sheikh Naim Qassem ya ƙara da cewa: rubuta wannan gado mai rai da tattara ayyukansa na baka da rubuce-rubuce, yana samar da tushen amfani mai zurfi ga masu bincike, jami'o'i da cibiyoyin dabarun kuma yana tabbatar da ci gaban tushen gwagwarmaya a fagen jama'a da kafofin watsa labarai.
Ya ɗauki makarantar jihadi ta Karbala wadda ta dogara kan sadaukarwa da tafarkin Imam Hussein (A.S) da mai isar da saƙo da tsararren gini na Sayyidaah Zainab (A.S) a matsayin tushen asali na horar da mutane masu 'yanci da tabbatar da haƙƙi a cikin al'umma kuma ya ƙara da cewa: shahidi Sayyid Hassan Nasrallah bisa dogaro daga waɗannan koyarwar da kalaman Imam Khomeini (Allah ya jikansa), ya bayyana al'adun Ashura ba wai kawai a kwanakin Muharram ba, a'a a duk rayuwarsa ta jihadi kuma ya samar da ingantaccen ƙarfi don fuskantar manyan ƙalubale kuma a wannan tafarki ya zamo tattarawa da ƙididdigewa ga nazarin tunaninsa da ayyukan shahidi Nasrallah a matsayin takardar tarbiyya ta shekarun da suka gabata wajibi ne na asali.
Sheikh Naim Qassem ya nanata: a gefen al'adun jihadi na Ashura, ya zamo tushen "wilaya da bin wilaya" ma ba a matsayin wani batu da ya bayyana, amma ba a matsayin sabon abu bas ai dai a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙai da ƙa'idodin asali na addini, da ke gudana kan tushen yunkurin al'ummar musulmo da jigon gwagwarmaya.
Babban Sakataren Hizbullah tare da ambaton wani babban kwamandan fagen gwagwarmaya ya ƙara da cewa: bai kamata mu manta abin da shahidi Haji Qassem Soleimani ya yi ba, shahidi Soleimani hakika babban mai goyon baya ne ga gwagwarmaya a duk yankin.
Sheikh Naim Qassem ya kuma ɗauki ficewar sojojin Amurka a matsayin nasara ga al'ummar Iraki kuma ya ƙara da cewa: ina gaisuwa ga al'ummar Iraki masu daraja, cibiyar addini, jagoranci da Hashdush-Sha'abi waɗanda da sadaukarwa da tsayin dakansu, suka kori mamayewar Amurka daga ƙasarsu.
Ya nanata cewa muna ganin 'yantar da kudancin Lebanon a gaban idanunmu ya ce: Isra'ila ba za ta iya zama a kudu har abada ba kuma gwagwarmaya da tsayin dakarta ta ƙirƙiri wani tarihin jarumta. Mafuta zata fara ne da ficewar maƙiya Sahayoniya da Amurka a kunyace waɗanda da duk ƙarfinsu ke tallafawa mamaye kan yankinmu.
Babban Sakataren Hizbullah ya nanata: a al'amuran cikin gida na Lebanon a shirye muke don haɗin gwiwa, amma ba tare da karɓar umarnin waje ba.
………………
Ra'ayinka