7 Faburairu 2017 - 09:30
Ansarullah Na Yemen Sun Harba Makamai Masu Linzami A Birnin Riyad

Mayakan kungiyar Ansarullah a kasar Yemen sun bayyana cewa sun harba makamin linzami zuwa birnin Riyar na kasar Saudia a karon farko

Kamfanin dillancin labaran SABA ta gwamnatin kasar ta Yemen  ta bayyana cewa makamin linzamin wanda aka cilla kimani kilomita 1000 daga zuwa birnin Riyad daga kasar ta Yemen ya fada kan wani barikin sojoji a birnin Riyad Babban birnin kasar Saudia, kuma mayakan na Huthi sun yi alkawarin cilla wasu makaman linzamin da dama a lokuta masu zuwa. 

Wannan wannan sanarwan dai kafafen yada labarai na cin gida sun tabbatar da cewa makamin linzami a karon farko daga kasar ta Yemen ta fada kan barikin sojoji na al-Mazahmiya kusa da birnin Riyad.

Gwamnatin kasar saudia dai har yanzun bata ce uffan kan lamarin ba, bata kuma musanta kan cewa makamin ya fada cikin a birnin ba. 

Tun cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne saudia take jagorantar kawancen sojojin kasar don dawo da tsohuwar gwamnatin kasar Yemen, amma har yanzun kimani shekaru biyu kenan ta kasa yin hakan. Kuma ya zuwa yanzu ta kashe mutane kasar yemen kimani dubu 11,400 mafi yawansu fararen hula.288