A karshan makon da ya gabata bayan amincewar Yahya Jammeh na ficewa daga kasar, sabon shugaba Adama Barrow ya yi kira ga ‘yan kasar na su koma gidajensu.
Duban mutane da furgaban tashin hankali ya tilastawa tserewa sun bayyana farin cikinsu na gani an lafar da kurar rikicin siyasar Gambia ba tare da Zub da Jinni ba.
Shugaba Adama Barrow da har yanzu ke Senegal ya nada wata tsohuwar ministan Yahya Jammeh, wato Fatoumata Jallow-Tambajang a matsayin mataimakiyar shugaban kasa.
Mai Magana da yawun shugaban kasar Halifa Sallah ya ce an zabi tsohuwar minister ne dan cike gibi ganin yadda nade naden da sabon shugaban kasar ya yi suka karkata gefe guda.
Al’amura dai sun soma dai-daita a rikicin siyasar kasar da ya ja hankalin duniya.288