Bayanai sun nuna cewa dan kunar bakin waken ya kai harin ne da mota a safiyar wannan Lahadin a harabar kasuwar kayan lambu dake birnin kamar yadda kakakin ma'aikatar cikin gida na kasar, Saad Maan ya tabbatar.
Ko baya ga wadanda suka rasa rayukansu akwai wasu 35 da suka raunana kamar yadda wata majiyar asibiti ta shaidawa kanfanin dillancin labaren AFP.
Har kawo lokacin fasara wadanan labaren babu wata kungiya data dau alhakin kai harin, saidai so tarin yawa akan danganta ire-iren wadanan ayyukan ta'addin ga kungiyar nan ta IS.