Majiyar Sojan Yemen ta ci gaba da cewa; Shida daga cikin 'yan koren Saudiyyar an kashe su ne a gabacin "Jabalul-Han' da ke yankin 'al-Dhubab' a gundumar Ta'az.
Majiyar ta ci gaba da cewa; wasu hudu daga cikin 'yan koren sun halaka ne a cikin garin 'al-salu' sai kuma mutum guda a tuddan 'al-wakil'
Manyan bindigogin sojoji da kuma mayakan sa kan kungiyar "Ansarullah' sun kai hari akan sansanin sojojin Saudiyya da ke al-huraiqah.
Tun a cikin watan Maris na 2015 ne Saudiyyar ta bude kai harin soja akan Yemen, wanda kawo ya zuwa yanzu ya ci dubban rayuka.288