Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayar da rahoton cewa, shugaba Vladimir Putin na Rasha da kuma shugaba Rauhani na Iran, sun tattauna kan matakai na gaba wajen yaki da ta'addanci a Syria, da kuma kokarin warware rikicin kasar ta hanyar siyasa.
Haka nan kuma sun tattauna kan zaman da za a gudanar a tsakanin bangarorin gwamnatin Syria da kuma 'yan adawa na siyasa, har ma da wasu wadanda suka dauki makami, wadanda suka amince su shiga tattaunawa ta siyasa a halin yanzu, zaman dai za a gudanar da shi a kasar Kazakistan.
Wannan dai shi ne karo na uku da shugabannin na Rasha da Iran suke tattaunawa ta wayar tarho a cikin 'yan kwanakin nan,a kan halin da ake ciki a Syria da ma wasu batutuwan na daban da suka shafi yankin gabas ta tsakiy.288