17 Disamba 2016 - 20:03
ECOWAS ta bukaci Jammeh ya mika mulkin Gambia

Shugabannin Kasashen Yammacin Afrika sun bukaci gaggauta kawo karshen rikicin siyasar Gambia, bayan Yahya Jammeh ya ki amincewa da shan kayi a zaben shugabancin kasar da Adama Barrow ya lashe.

Shugabannin sun bukaci haka ne a taron ECOWAS na 50  da suka gudanar a birnin Abuja na Najeriya, in da suka mafi mayar da hankali kan rikicin siyasar Gambia.

Tuni dai Jammeh ya shigar da kara a kotun koli don kalubalantar sakamakon wanda ya amice da shi a farko kafin ya bijire daga bisani.

A farkon makwannan ne dakarun Jammeh suka kwace hukumar zaben kasar, abin da ya janyo masa suka daga kasashen duniya.288