7 Disamba 2016 - 19:28
Ana ci gaba da nuna rashin yarda da matsayar gwamnatin Kaduna akan Harkar Musulunci

Tun bayan lokacin da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar abin ta kira Farar Takarda, inda ta fito fili ta kira Harkar Musulunci a Nigeria a matsayin kungiyar 'yan tawaye, ake ta samun martani na nuna rashin yarda da wannan matsaya ta gwamnatin jihar ta Kaduna daga bangarorin al'ummar musulmi, da sauran kungiyoyi na al'umma.

A ciki da wajen Nigeria.

Kungiyoyin Kare hakkin musulmi a cikin kasa kamar kungiyar MURIC, samarin kungiyar mabiya addinin Kirista CAN da sauran kungiyoyin kare hakin bil adama a ciki da wajen Nigeria duk sun yi wannan martanin, inda suke bayyana matsayin su game da Harkar Musuluncin a Nigeria a matsayin ta na Harkar addinin musulunci data kwashe shekaru tana kira zuwa ga kyawawan dabi'u da komawa zuwa ga addinin Allah subhanahu Wa Ta'ala.

Haka nan kuma sun yi amfani da sanin su ga jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky na irin hakurin sa da ilimin sa da hangen nesan sa kan dukkanin matsaloli da ke jewa su dawo, da kuma irin tsayuwar dakan sa wajen kare jinin al'umma a lokuta masu hadari, da cewa wannan masaniyar tasu game da shi tun da jimawa ta karyata dukkanin abin da gwamnan Kaduna yake kokarin yayatawa.

Al'ummar musulmi sun zura ido su ga yadda ake Karen tsaye ga dokoki da kuma tankwara gaskiya don cimma muradi na duniya.

Sai dai dama Bahaushe yana cewa karya fure take.288