Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wata ganawa da yayi da masanan kasar Iran a birnin New Delhi a yau Asabar a ci gaba da ziyarar da yake yi a can inda ya ce matukar Amurka da sake dawo da takunkumin da ta sanya wa Iran, to kuwa Iran ba za ta ci gaba da girmama yarjejeniyar nukiliya din ba.
Minista Zarif yana mayar da martani ne ga kuri'ar da majalisar Amurka ta kada na sake tsawaita takunkumin da Amurkan ta sanya wa Iran har na tsawon shekaru 10 masu zuwa da suka hada da takunkumi kan bankuna da kuma bangaren makamashi da masana'antu na tsaron kasar, inda ya ce sake tsawaita wannan takunkumin yana nuni da cewa gwamnatin Amurka ba abar dogaro ba ne.
Tun dai bayan kada wannan kuri'a da majalisar Amurkan ta yi, 'yan majalisar Iran ma suka fara tsara wani kudurin doka da zai tilasta wa gwamnatin kasar komawa da ci gaba da ayyukan nukiliyan da kasar ta ke yi wadanda ta dakatar da su saboda yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma din.288