Tashar television ta Presstv a nan Tehran ta nakalto hukumar UNICEF tana fadar haka a yau Lahadi ta kuma kara da cewa yaran suna rayuwane a yankunan da hukumar ba zata iya kai masu taimako ba ko kuma suka karkashin ikon kungiyoyin yan ta'ada. UNICEF ta kara da cewa 100,000 daga cikinsu suna karkashin ikon kungiyar yan ta'adda a birnin Halab na kasar ta Siria.
Babban Directan hukumar Anthony Lake ya ce yara a wadan nan yankuna basa zuwa makaran bata samun abinci mai gina jika , hatta wasu lokutan ma basa iya was don tsoro.
Anthony Lake ya ce a makonnin da suka gabata daliban makaranta da dama suka rasa rayukansu a wani harin da yan tawaye suka kai a cikin birnin Halab wanda a halin yanzu rabinsa yana karkashin ikon yan ta'adda.288