Sarkozy ya sha kaye daga hannun tsofin Firaministan kasar guda biyu Francois Fillon da Alain Juppe wadanda zasu fafata a zagaye na biyu dan samun wanda zai tsayawa Jam’iyyar su takarar.
Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya zo na uku ne a zaben fidda gwanin da kashi 21 yayin da tsohon Firaministan sa Francois Fillon ya zo na farko da kashi 44 sai kuma Alain Juppe da ya zo na biyu da kashi 28 na kuri’un da aka kada.
Sarkozy ya bayyana goyan bayan sa ga takarar Francois Fillon, kuma nan take ya bayyana cewar zai janye daga harkokin siyasa.
Tsohon shugaban ya shaidawa magoya bayan sa cewar yayi iya bakin kokarin sa amma kuma hakan bai sa ya janyo ra’ayin maus zaben ba.
A karshen wannan mako ne za’a gudanar da zaben zagaye na biyu tsakanin Francois Fillon da Alain Juppe.288