Misis Cliton wace ta bayyana hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho ga kwamitin yakin neman zaben ta ce akwai abubuwa da dama da suka zama sila na shan kayen ta a zaben da aka gudanar a ranar takwas ga watan nan.
Clinton ta ce sanarwar da Mista Comey ya yi kan batun amfani da Email din ta a lokacin da ta ke Sakatariyar harkokin waje, kwanaki biyu gabanin zabe shi ya rage mata magoya baya.
Wadanan kalamen na Misis Cliton na zuwa ne a daidai lokacin da dubban Amurkawa ke ci gaba da boren kin amincewa da zababen shugaban kasar Donalt Trump.
A birnin New York 'yan sanda sun yi kokari hana masu zanga-zangar isa dandalin Union, da wasu kuma na daban da suka tunkari gidan na Mista Trump.288