Jami'ai masu kula da hubbaren Askarain da ke Samarra, su sanar da cewa; Harin na jiya lahadi an kai shi ne da wata mota da aka makare da abubuwa masu fashewa.
Motar ta tarwatse a daidai wurin da ake ajiyar motoci. Adaidai lokacin da masu ziyarar ke tafiya domin isa hubbaren a kafa, wani bom ya tashi a tsakiyar mutane. Adadin wadanda su ka rasa rayukansu sun kai 10, yayin da wasu 30 su ka jikkata.
Mafi yawancin wadanda harin na Samarra ya rutsa da su dai Iraniyawa ne.
A kudancin garin Takrita ma dai an kai wani harin da motar da aka makare da bama-bamai da ya yi sanadin mutuwar fararen hula 7 da kuma jikkata wasu 15.