26 Oktoba 2016 - 19:53
Wata Kotun Daukaka Kara A Kasar Masar Ta Tabbatar Da Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Mohammad Badee

Wata kotun daukaka kara a kasar Masar ta tabbatar da hukuncin daurin rai da rai kan shugaban kungiyar Ikhwanul Muslimin wacce aka haramta

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bayyana cewa a yau Laraba ne kudun daukaka karar ta tabbatar da wannan hukuncin kan Badee da kuma wasu mutane 36 kan laifin kisan kai da kuma tada hankali.

Kutun ta ki amincewa da bukatar Badee na ta sake duba hukuncin da aka yanke masa, banda haka kotun ta tabbatar da hukuncin kisa kan mutane 10 wadanda basa hannu. 

Wata kotun hukunta manya manyan laifuffuka ce ta yanke hukuncin shekaru biyu da suka gabata kan mutanen 36. Jamillan mutanen da aka gurfanar a kan wannan laifin dai sun kai 47 kuma daga cikinsu akwai jami'an gwamnati da kuma ministocin gwamnatin Mohammad Mursi wacce shugaba Abdul fata Sisi ya yiwa juyin mulki a shekara ta 2013.