Limamin Juma'ar Tehran ya yi tir da shirun da kasashen duniya su ka yi akan laifukan yakin da Saudiyya ta ke yi a Yamen.
Hujjatul-Islam Wal-Muslimin Kazim Sadiqy, ya yi ishara a cikin hudubarsa ta juma'a da laifukan yakin da Saudiyya ta ke tafkawa a kasar Yamen,musamman kashe kananan yara da kuma harin bayan nan da ta kai a wurin ta'aziyya.
Limamin na Tehran ya kwatanta kisan da Saudiyyar ta ke yi wa kananan yara a Yamen da irin wanda Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta ke yi wa Palasdinawa.
Har ila yau, limamin Tehran din ya ambaci atisayen da sojojin saman Iran su ka yi a karo na 6, sannan ya ce; Sako ne na kawance ga al'ummun wannan yankin, a lokaci daya kuma gargadi ne ga masu adawa da Iran.288