A ganawarsa da tashar talabijin na NBC ta kasar Amurka: Shugaban kasar Iran Sheikh Hasan Ruhani ya bayyana cewa; Iran tana sanya ido kan rikicin kasar Siriya tare da tabbacin cewa; ta hanyar lumana ce kadai za a kai ga warware rikici da dambaruwar siyasar kasar.
Har ila yau Shugaban kasar Iran ya mai da martani kan bukatar sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ta nema dakatar da shawagin jiragen saman yakin kasar Rasha da na Amurka a yankunan arewacin Siriya; Yana mai cewa manufar Kerry ita ce bai wa 'yan ta'adda damar kai komo a yankin domin jiragen saman yakin Rasha tana kai musu hare-hare babu kakkautawa.288