14 Satumba 2016 - 13:51
Boko Haram Ta Ce Zata Cafke Shugaban Najeriya

A wani sabon faifan bidiyo data fitar kungiyar Boko Haram ta ce za ta cafke shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Bidiyon na mintina 13 wanda aka dauka a wani boyayyen wuri ya nuna mayakan na gudanar da sallar idin babba sallah a ranar litinin data gabata. 

Kungiyar a karkashin jagorancin Abubakar Shekau ta ce, da yardan Allah za ta kama shugaba Buhari wanda ta bayyana shi a matsayin kafiri da hannunta.

Sai dai a wannan karon ma, jagoran  kungiyar, Abubakar Shekau bai bayyana a cikin bidiyon ba in da mataimakinsa ya isar da sakon. 288