A daren jiya ne shugaba Vladimir Putin ya sanar da bukatar kasarsa na janye dakarunta daga Syria, kamar yadda dai aka ji labarin shiga yakin kwatsam a farko haka aka ji labarin janyewarta daga Syria, bayan watanni 4 da Rasha ta kwashe tana luguden wuta akan mayakan 'yan ta'adda da suka hana zaman lafiya a Syria
Mr Putin wanda ya sanar da matakin janye dakarun yace hakan shine daidai ganin haka ta cimma ruwa a kokarin Rasha na tarwatsa kungiyoyin ‘yan ta’dda
Yanzu haka ma dai tawagar Majalisar Dinkin Duniya da bangarorin dake rikici da juna a Syria sun koma zaman tattauna hanyoyi kawo karshen rikicin na Syria a birnin Geneva
Shekaru sama da 4 aka kwashe ana fama da tashe tashen hankula kuma mutane sama da 300,000 ne suka rasa rayukansu baya ga miliyoyi da suka tsere daga muhallinsu.288