Shugaban kasar Ivory Coast Alhasana Watara ya yi kira ga kasashen yankin yammacin Afrika su kafa rundunar yaki da ayyukan ta'addanci. Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya nakalto shugaban yana fadin haka a jiya Litinin bayan wasu hare haren da yan ta'adda suka kai a kan wasu wuraren saukar baki ya kasashen waje guda ukku a kusa da birnin Abidjan a ranar lahadi da ta gabata. Hare haren dai sun rutsa da wasu yan kasashen waje, da kuma wasu yan kasar su 21. Har'ila yau yan ta'addan da suka kai hare haren guda ukku su ma sun rasa rayukansu a cikin harin.
Kungiyar Alqaeda reshen Magrib ta dauki alhakin kai wadan nan hare hare a wani shafin Telegarph da suka bude.288