Bayanai daga Lome na cewa mutane sun fito a wasu sassan kasar domin tafiya rumfunar zabe.
Akwai 'yan sanda kusan dubu tara da wasu sojoji dake sintiri a koina cikin kasar.
Hukumomin kasar sun rufe kan iyakoki domin gudun kada ayi masu kutse.
Shugaban kasar mai ci Faure Gnassingbe mai shekaru 48 ya maye gulbin mahaifin sa ne da ya mutu tun shekara ta 2005.ABNA