Muzahara
Muzahara
Muzahara
Wannan Muzahara dai an somo ta ne daga Gwargwaje cikin birnin kuma an kammala ne a filin Husainiyar Baqiyyatullah.
Tun da aka fara Muzaharar dai gungun sojoji cikin motoci Bus-bus da motoci masu sulke da bindigogi suka rika bin muzaharar, wannan dai bai sa aka canza muzaharar kamar yadda aka tsara ba.
Mahalarta sun rika rera take da daga tutoci masu dauke da yabon Sayyidah Zahra[SA], haka nan kuma wasu sun rika gabatar da tamsiliyyah na kamanta rayuwar Sayyidatu Nisa'il Aalameen Sayyidah Zahra[SA].
Bayan isowa filin da aka kammala sai wani bangare na Harisawa suka gabatar da Fareti na musamman sannan Malama Zeenatuddeen Ibraheem ta fara gabatar da jawabin rufe muzaharar.ABNA