Jega wanda ya amsa tambayoyi game da zaben a Abuja, ya ce za su yi "iyaka kokarinsu domin tabbatar an yi zabe cikin gaskiya da adalci a ranar 28 ga watan Maris."
"Masu zabe sun karbi katunan dindindin fiye da miliyan 56 daga cikin mutane miliyan 67.8 da suka yi rijista," in ji Furofesa Jega.
Ya kara da cewa "har yanzu akwai katunan zabe na dindindin guda 700,000 da ba a buga ba."
"Ana ta yin rade radin cire ni. Hakan bai dame ni ba. Aikina kawai nake yi," Jega ya jaddada. ABNA