Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti{A.S}-abna-shugaban Ansarullahi na Yaman a wata hira da yayi da manema labarai a garin Sa'ada yace, hudar kasar Yaman da sauran kasashe ya ginu ne a bisa tsari na girmama juna da rashin tsoma baki ga al'amuran da suka shafi cikin gida.
Abdulmailik Husi ya kara da cewa, muna farin ciki a bisa huda da kowace kasa ta larabawa ko ta musulmi tare da girmama juna da rashin shiga al'amuran da suka shafi siyasar kasar.
A wani bangaran ya yi tsokaci a bisa taimakon da wasu kasashe ke yima tsohon shugaban kasar wato Mansur Hadi domin kawo cikas ga tattaunawar kasa dake gudana a yanzu.ABNA