5 Maris 2015 - 17:07
An ‘yanto jami’in Difilomasiyar Iran da a ka  sace a Yaman

Jami’in Difilomasiyar Iran wanda ‘yan ta’adda suka sace a San’a na kasar Yaman sama da shaikara daya da rabi da suka wuce, a yau ne ya isa birnin Tehran bayan an ‘yanto shi daga hannun ‘yan ta’adda

Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti{A.S}-abna-Noor Ahmad Nikbakht jami’in Difilomasiyar kasar Iran a Yaman an sace shine a kan hayarsa ta zuwa wurin aiki kuma aka nufi wani wurin da ba’a sani ba.

Ma’aikatar tsaro ta Jamhuriyar musulunci tare da hadin gwiwar dakarun kare juyin juya hali na Iran awani samame da suka kai a maboyar ‘yan ta’addar dake wajen Yaman dakarun sun samu  nasarar kwato jami’in daga hannun ‘yan ta’adda kuma ayau ne ya iso Tehran babban birnin Iran.

Ma’aikatar tsaro ta Iran ta aika sakon taya murna ga iyalan jami’in da kuma jagoran juyin musulunci na Iran a bisa wannan gagarumar nasarar.ABNA