2 Maris 2015 - 06:25
Sabon zagaye na tattaunawar nukiliyar Iran a Switzeland

Ayaune ministan harkokin kasashen waje na Iran ya isa Geneva na Switzerland domin ganawa da takwarorin aikinsa na kasashen turawa agefe daya kuma zai gana da John Kerry takwaran aikinsa na Amurka a cigaba da tattaunawar da suke na makamashin nukiliya na Iran.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti{A.S}-abna-ministan harkokin kasashen waje na jamhuriyar musulunci ta Iran bayan ya gabatar da jawabi a kwamitin kiyaye hakkin bil’adama na majalisar dinkin Duniya, zai kuma gana da ministocin kasashen Holan da na Rasha.

Agefe daya kuma Zarif zai gana da John Kerry ministan harkokin kasar waje na Amurka a sabon zagaye na tattaunawa game da makamashin nukiliya na Iran, shugaban makamashin nukiliya na Iran Salihi yana cikin ‘yan tawagar da suke ma Zarif rakiya.ABNA