Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: A jawabinsa, Jagora (H) ya bayyana samartaka a matsayin lokaci mai matuƙar muhimmanci a rayuwar mutum, inda ya yi kira da a yi amfani da shi wajen ayukka muhimmai da ibadodi. Ya ce, “Lokacin samartaka ba wai kawai shekaru ne ba, a’a, ƙumaji da aiki ne.”
Shaikh Zakzaky (H) ya yi tsokaci kan wasu ra’ayoyin shakku da ake yaɗawa game da tabbatar da addini, misalin masu cewa tabbatar da addini ba zai yiwu ba saboda ƙarancin ƙarfi ko kasancewar ba kowa ne Musulmi ba. Ya ce, tabbatar da addini ba yana nufin sai kowa ya zama Musulmi ko Shi’a ba ne. Ya ƙara da cewa, gwagwarmayarmu ba kira ne zuwa ga Shi’a ba, kira ne ga tabbatar da addini.
Ya bayyana cewa, tabbatar da addini na nufin ɗaukaka dokar Allah a kan kowace doka, ta yadda ba za a samar da dokar da ta saɓa wa ta Allah ba. “Nizamin Musulunci shi ne nizamin da ba zai saɓa ma na Allah ba.” Ya kawo misalan Shehu Ɗanfodiyo da kuma ƙasar Iran, inda akwai waɗanda ba Musulmi ba, har da Yahudawa a Iran. Ya ce, ba sharadi ne sai kowa ya zama Musulmi ba kafin tabbatan addini.
A ƙarshe, Jagora (H) ya jaddada cewa, yunƙurin maƙiya na murƙushe gwagwarmaya ba zai yi nasara ba, kuma nasara za ta kasance ga ƴan gwagwarmaya, in sha Allah. Ya yi kira kan mutum ya tsayu ƙyam tare da goyon bayan gaskiya, ba ɗan zura ido ko kallo ba, don ganin addini ya tabbata.
Daga Ofishin Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
06/Jimada ula/1448
17/10/2026
Ra'ayinka