Ministan tsaron kasar, Jean-Yves Le Drian, ya ce za su tsaurara tsaro a yankunan da ya ce "suna da matukar muhimmanci."
Ya ce kara da cewa rabin jami'an tsaron za su kare makarantun Yahudawa guda 700.
Fira Ministan kasar, Manuel Valls, ya ce tabbas Amedy Coulibaly -- dan bindigar da ya kashe mutane hudu a wata kasuwar Yahudawa -- yana da abokan da suke taimaka masa.ABNA