30 Disamba 2014 - 11:34
An gano wasu motoci da saudiya ta ba Da'ish{isil}

Motocin da sojojin Iraki suka kama a matsayin ganima daga kungiyar isil{da'ish} a kewayen garin takrid na dauke da Lambobin kasashe larabawa ne.

Tasakar labarai ta Ahlulbati{a.s}-abna-{Ali karim Alhusnawi} kwamandan fataliyar malik ashtar Iraki yace; mun samu dalilai masu karfi dake nunin hannuwan wasu kasashe larabawa dake makwaftaka da Iraki a wajen taimakama yan ta'adda a yammacin takrid na Iraki.

Ya kara da cewa; motocin da sojojin Iraki suka kama na yan kugiyar Isil a yankin takrid na dauke da lambobin wasu kasashen larabawa wanda a saman lambar ba a rubuta{ na fitarwa ne}ba wato akasashe ne kadai ake amfani dasu aba ayarda afita dasu zuwa wasu wurare ba.

An rawaito cewa Alhasnawi yace lambobin motocin na kasae saudiya ne sa jodan da kuma yankin da yan ta'adda suka kama a syria, motocin dai masu dauke da kayan fada an tura sune domin taimakama yan ta'adda na Da'ish.

Acewar sa sakamakon kungiyoyin leken asiri na saudiya,joda,turkiya, kuma da hadin kan na Amurka da isra'ila a yankin sune suka haifar da kungiyoyin yan ta'adda na Da'ish {isil}.ABNA