29 Nuwamba 2014 - 10:27
Togo:An Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati A Birnin Lome

Al’ummar kasar Togo na ci gaba da gudanar da zanga-zangar kyamar tazarce da shugaba Gnassingbe ke neman yi.

Kamfanmin dillancin labarai na kasar Faransa ya habarta cewa a jiya juma’a dubun dubutan Al’ummar birnin Lome ne suka gudanar da gagarumar zanga-zanga domin nuna adawar su da kudirin shugaban kasar Faure Gnassingbe na zartewa a kan karagar milki.  

Mahalarta zanga-zangar sun bukaci shugaban kasar da ya janye kudirinsa na tsayawa takara karo na uku a zabe shugabancin kasar mai zuwa, wanda za’a gudanar a shekara ta 2015 mai kamawa.

wannan zanga-zanga ita ce ta uku da Al’ummar birnin na lome ke gudanar kalkashin kiran da shugaban jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula suka kira, har ila yau sun dauki kudirin cewa za su ci gaba da wannan zanga-zanga har lokacin da za a gudanar da zaben shugaban kasar.

Daga nasu waje, jami’an ‘yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa mahalarta zanga-zangar. ABNA