Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a zaman da bangarorin siyasar kasar Burkina Faso suka gudanar jiya tare da wakilan kungiyoyin farar hula da kuma na manyan kabilun kasar, sun cimma matsaya tare da sojoji kan kafa majalisar shawara ta kasa da za ta jibinci lamurran gudanarwa a kasar, wadda farar hula zai jagoranta, tare da mambobi 90 daga kowane bangare.
Rahoton ya kara da cewa shugaban majalisar zai ayyana Firayi ministan kasar, wanda zai jagoranci majalisar ministoci, wadda za ta kunshi ministoci 25 dukkaninsu farar hula, wanda hakan zai bayar da damar yin tsare-tsaren da suka kamata kafin mika mulki ga farar hula baki daya a shekara mai zuwa. ABNA