11 Nuwamba 2014 - 15:11
Shugaban Kasar Syria Ya Ce Zai Dubi Shawarar Tsagaita Bude Wuta Da Yan Tawayen Kasar

Shugaban kasar Syria Bashar Alasad ya yaba da shawarar da jakadan majalisar dinkin duniya kan rikicin na Syria Staffan de Mistura ya gabatar a jita litnin na dakatar da bude wuta tsakanin sojojinsa da yan tawayen kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Syria ya nakalto shugaban yana fadar haka a jiya a lokacinda yake ganawa da tawagar mDD kan rikicin kasar ta Syria a birnin demascus.

Staffan de Mistura, ya bukaci shugaba ya duba yiyuwan tsagaita bude wuta tsakanin bangarorin biyu daga yankunan arewacin kasar, musamman birnin Halab. Staffan de Mistura ya ce yana fatan hakan zai zama masomin warware rikicin na kasar ta syriana. ABNA