10 Nuwamba 2014 - 15:27
Rundunar Sojin Libiya Ta Zargi Gidan Sarautar Qatar Da Taimakawa Ta'addanci A Kasar Libiya

Babban hafsan hafsoshin sojin Libiya ya zargi gidan sarautar Qatar da taimaka wa kungiyoyin tsoffin ‘yan tawayen kasar masu tsaurin ra’ayin addinin Islama da makamai.

Kanal Abdur-Razzak Nadhuri babban hafsan hafsoshin sojin kasar Libiya ya bayyana cewar mahukuntan kasar Qatar sun aiko da jiragen sama dauke da tarin makamai da na’urori ga tsoffin kungiyoyin ‘yan tawayen Libiya masu tsaurin ra’ayin addinin Islama da suke tada da kayar baya a kasar.

Nadhuri ya kara da cewar rundunar sojin Libiya zata ci gaba da kokarin ginin ta ‘yantar da dukkanin kasar ta Libiya daga mamayar masu dauke da akidar kafirta musulmi, sai dai matsalar har yanzu kasashen da suke kawance da Libiya ba su taimaka mata yadda ya dace.  ABNA