13 Oktoba 2014 - 18:48

Hukumar lafiya ta kasar Libya ta bayyana cewa, cikin 'yan kwanakin da suka gabata, sama da mutane 21 ne suka mutu kana wasu 60 suka ji rauni a wani kazamin fada tsakaninsu 'yan tsagera da sojoji a garin Kikla da ke yammacin Tripoli, babban birnin kasar.

Wani kwamandan mayakan sa kai na Zintan wadanda ke goyon bayan kungiyar bin tunanin gargajiya ya bayyana cew, mayakansu sun fara kai hari a garin Kikla mai tazarar kilomita 150 daga birnin Tripoli, wanda ke karkashin dakarun Fajr Libya mai goyon bayan kungiyar bin addinin musulunci. Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Libya JANA ya bayar, an ce, mazauna wuraren da ke yammacin Tripoli da dama sun tsere daga muhallinsu domin gujewa hargitsin. ABNA