Rahotanni sun ce sojin Turkiya sun girke tankunna yaki da makaman roka a garin Mursitpinar wanda ke kusa da garin Kurdawan Ain al Arab, bayan wasu jerin harsasai sun samu kauyukan dake cikin kasar ta Turkiya.
Kakakin Majalisar kasar Cemil Cicek yace a yau talata suke saran gwamnati ta gabatar da kudirin daukar matakin soji.
Baya ga kasar ta Turkiya kasashen larabawa da dama ne suka dafawa kasar Amruka da kawayenta baya wajen yakar yan kungiyar mujahidan dake fafatukar kafa daular musulunci a kasashen Iraki da Siriya ISIS
Kasashen dais un hada da Saudiya, Imarat Arba, Qatar, Jordan da kuma Bahren ABNA