24 Satumba 2014 - 20:27

'Yan ta'addan ISIS sun rusa wani babban masallaci mai tsawon tarihi da ake kira masallacin Arba'in da ke cikin garin Tikrit a lardin Salahuddin da ke arewacin kasar Iraki.

Kamfanin dillancin labaran Saumariyyah News ya bayar da rahoton cewa, 'yan ta'addan sun tarwatsa masallacin ne baki daya a yau bayan da suka dasa wasu nakiyoyin a cikinsa, kuma suka yi amfani da na'urorin tayar da bama-bamai daga nesa wajen rusa shi, masallacin dai ya kasance daya daga cikin masallatai mafi dadewa a kasar Iraki da aka gina shi tun lokacin tabi'ai.

 

'Yan ta'addan ISIS dai sun rusa masallatai da wuraren ibada da dama  a cikin kasashen Iraki da Syria, da hakan ya hada har da kabrukan annabawa da na sahabbai da sauran bayin Allah, lamarin da malaman addinin muslunci a kasashen daban-daban da suka hada hard a na babbar jami'ar muslunci ta Azahar da ke Masar suka bayyana hakan da cewa ba addinin muslunci ba ne. ABNA