Mbabazi na daga cikin manyan hafsosin sojin da suka yi juyin miki a kasar wanda shine ya baiwa shugaba Yoweri Museveni damar darewa kan karagar milkin kasar ta Uganda, tsofon na hanun damarsa kuma daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar NRM mai milki a kasar inda tun bayan kafa jam’iyyar shi ke rike da mikamin babban sakataren jam’iyyar , kafin nadasa a matsayin Piraminista a shekara ta 2011, Mr Amama Mbabazi ya kire mikamin Ministan tsaron kasar daga bisani ya koma Ma’aikatar tsaro.a watan Maris din da ya gabata shugaban kasar Museveni a matsayinsa na shugaban jam’iyyar ya tsige Mbabazi daga matsayinsa na babban sakataren jam’iyyar inda tun daga wannan lokacin ne manazarta ke ganin cewa a kwai sabani tsakanin magabatan, bayan tsige shi daga mikamin piraministan, hakan ya tabbatar da cewa a kwai sabani tsakanin tsaffin abokanan biyu.
Wata majiya na ganin cewa sabanin ya kunno kai tun bayan wani kudiri da Majalisar dokokin kasar ta zartar na cewa shugaba Museveni shi ne dan takara daya tilo a zaben shugaban kasar na 2016 ganin cewa Jam’iyyar ta sa ita ce jam’iya wacce tafi ko wace jam’iya yawan kujeru a Majalisar dokokin kasar.
Shugaba Museveni dai ya dare kan karagar milki tun a shekara ta 1986, wanda kuma yake son meda shugabancin kasar ta Uganda tamkar masarauta, idan ya lashe wannan zabe zai zamanto daya daga cikin shugabanin da suka fi dadewa a kan karagar milki a Nahiyar Afirka inda zai kwashe fiye da shekaru 30 a kan karagar milki.
Duk da cewa shugaba Museveni yayi ta lashe zabe a zabukan da suka gabata, saidai jam’iyyun adawar kasar sun yi ta zarkin jam’iyar sa da tabka magudi tare da rashin gudanar zabe cikin tsari.
Masu nazari kan harakokin siyasar kasar na ganin cewa duk da cewa tsohon Piraministan bai fito fili ba ya bayyana sha’awar na tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben 2016 ba, amma a kwai kishin kishin hakan, wanda shine ma ya janyo sabani tsakaninsa da shugaban kasar har ya cike shi daga kan kujerar sa ta Piraminista. ABNA