Majiyoyin hukumar Hilal Ahmar a kasar ta Libya sun ce dukkanin mutanen da suka rasa rayukansu suna cikin wani karamin jirgin ruwa ne da ya kife da su a ranar Juma'ar da ta gabata, a lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa nahiyar turai ta barauniyar hanya, inda aka tseratar da 'yan kalilan daga cikinsu, sauran kuma suka nutse cikin ruwa.
Tun kafin wannan lokaci dai masu hankoron shiga nahiyar turai daga wasu kasashen Afirka har ma da wasu na Asia, sukan tsallaka daga kasar Libya zuwa nahiyar turai, amma lamarin ya kara ta'azzara bayan kifar da gwamnatin marigayi Gaddafi, sakamakon halin da kasar ta Libya ta shiga na rashin doka da oda, da kuma barin gabar ruwan kasar ba tare da sanya ido ba. ABNA