Daga cikin yankunan da ambaliyar ruwan ta shafa har da Khartum babban brinin kasar.
Kwamiti mai kula da ambaliyar ruwa a Jahar Nahru Nil dake arewacin kasar ya ce ambaliyar ruwan ta rusa gidaje fiye da dubu guda tare da cinye filin noma fiye da Hekta dubu 12 a jahar
Har ila yau ambaliyar ruwan ta tafi da abinci mai dunbun yawa, bayan da ya rusa Makarantu, dakunan shan magani, massalatai, guraren ibada da saurensu.
Ya zuwa yanzu dai ba a tantance ba dukkanin asarar da ambaliyar ta janyo saidai shaidun gani da ido sun ce ambaliyar ruwan ta lashe rayukan Mutane akalla guda 10. ABNA