30 Yuli 2014 - 08:01

Majiyar mayaka masu kishin addini a kasar Libya ta bada sanarwar cewa sun kwace iko da barikin sojoji mafi girma a birnin Bengazi birnin Mafi girma a gabacin kasar a yakin da suke fafatawa da magoya bayan tsohon Janar na sojan kasar Khalifa Haftar a jiya talata

Majiyar sojojin kasar ta Libya ta tabbatar da labarin cewa bayan fafatawa na kwanaki masu yawa a jiya Talata mayaka masu kishin addini a birnin Bengazi sun kwace iko da barikin sojoji mafi girma a cikin birnin.

Har’ila yau wasu labaran sun yi nuni da cewa mutanen kasar Sudan 8 ne suka rasa rayukansu a unguwar Alkareemiyya da ke birnin Tripoli babban birnin kasar ta Libya a jiya.

Kamfanin dillancin labaran DPA ya nakalto shafin yanar gizo na jaridar Sudan Tribune a bugunta na jiya talata tana cewa, jimi’an ofishin jakadancin kasar Sudan da ke birnin Tripoli sun tuntubi dangin mamatan don shirin yi masu jana’iza.

Majid Sawar, jami’i mai kula da yan kasar sudan da ke aiki a kasashen waje ya bayyana cewa ya zuwa yanzu yan kasar ta sudan 10 ne suka rasa rayukansu a rikicin na kasar Libya. ABNA