30 Agusta 2026 - 18:46
Source: ABNA24
Jagoran Juyin Juya Hali: Mahukuntan Yankin Su Gane Makiyansu Na Gaskiya / Dukkan Al’ummu Kada Su Bari A Sami Sabani A Tsakaninsu

Jagora Ayatullah Sayyid Mujtaba Hosseini Khamene'i, jagoran juyin juya halin Musulunci, a cikin wani sako don tunawa da Makon Hadin Kai, ya taya al'ummar Iran da al'ummar Musulunci murnar ranar haihuwar Annabi Muhammad Mustafa (SAW) da Imam Ja'afar Sadiq (AS).

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Mai girma Ayatullah Sayyid Mujtaba Hosseini Khamene'i, jagoran juyin juya halin Musulunci, a cikin wani sako don tunawa da Makon Hadin Kai, a taya al'ummar Iran da al'ummar Musulunci murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad Mustafa (SAW) da Imam Ja'afar Sadiq (AS), ya bayyana shirin makiya Musulunci na nuna bambance-bambance don raunana al'ummar Musulunci da mamaye ta, kuma ya nuna cewa bayan an yaye lullubin fuska daga fuskar aikata laifuka na Amurka, ya zama wajibi ga al'ummar Musulunci su hadu don kare juna a gaban kafirci da kuma hada kai a fannoni daban-daban na rayuwa, kuma ya jaddada wa mahukuntan kasashen Musulunci: "Mahukuntan masu ta’addanci na Amurka da tsarin karya na sahyoniyya su ne tsantsan makiya na gani kasheni wajen kin hadin kan Musulunci da dukkan al'ummar Musulunci, ciki har da al'ummomin yammacin Asiya da arewacin Afirka, don haka ku gane makiyinku na gaskiya ku tunkari makircinsu."

Jagora ya kuma yi nuni da cimma nasarar da aka samu na darussan hadin kai na addinin Musulunci a Iran, yana mai sake ba da shawara ga al'umma da kada su bari a sami wani sabani a tsakaninsu.

Tarjamar Sakon Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci:

Bismillahir Rahmanir Rahim

"Muhammad Manzon Allah ne, kuma wadanda suke tare da shi, masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama a tsakaninsu."

بسم‌الله الرّحمن الرّحیم

مُحمّدٌ رَسولُ ‌الله وَالّذینَ مَعَهُ اَشِّداءُ عَلی الکُفّارِ رُحَماءُ بَیْنَهُم 

Ina taya al'ummar Iran masu daraja da al'ummar Musulunci murnar zagayowar ranar haihuwar hasken mafi girma, mafi darajar halitta, haske mai haskakawa, zaɓaɓɓen Allah, birnin ilimi, Annabin Rahma ga duniya, Manzon Musulunci (SAW), da ɗansa mai tsarki, Imam Ja'afar Sadiq (AS).

Tun lokacin da ranar Annabi ta bullo a Makka, hangen nesa na farin cikin ɗan adam da ke dogaro da kamalar ibada da biyayya ga Allah, ya sami wani haske na daban; ruhohin annabawa da mala'iku da tsarkaka sun nutsu cikin farin ciki, kuma shaidanun aljanu da mutane suka ciji yatsunsu na fushi da baƙin ciki. Domin mafi kyawun halittun Allah a duk duniyoyi marasa iyaka, ya bayyana a duniyar nan, kuma da sannu zai fara aikin annabci da hatimin annabci, yana riƙe da Alkur'ani mai girma da aikin shiryar da ɗan adam gaba ɗaya, don ya jagoranci ayarin ɗan adam zuwa ga ibada da kamala zuwa ga Allah. Rayuwar Annabi da wasiyyansa masu tsarki, duka darussa ne na shiriya da ibada, darussa na sanin Allah da ƙauna, darussa na akida da jihadi, darussa na rayuwa da kyawawan halaye na mutum da na al'umma, darussa na amana da gaskiya, darussa na 'yancin kai da mutunci, darussa na ilimi da aiki, darussa na rahama da tsauri, darussa na adalci da daidaito, da darussa na hadin kai da 'yan'uwantaka. Idan aka koyi waɗannan darussa da kyau kuma aka yi aiki da su, samun kololuwar farin ciki da jin daɗi zai zama mai sauƙi ga 'ya'yan ɗan adam. Mun yi imani cewa ruhun Annabin Rahma da ruhohin wasiyyansa da hujjoji masu tsarki, koyaushe suna kula da shiryarwa da tausayi ga yanayin Musulmai da al'ummar Musulunci. Lokacin da wani kuskure ya faru daga 'ya'yan wannan uba mai tausayi, ruhunsa yana jin ba dadi, kuma duk lokacin da Musulmai suka yi aiki da darussa da umarninsa, zuciyarsa mai tsarki tana farin ciki.

Yanzu Musulunci da mabiyansa, bayan sun shafe shekaru masu wahala da cikas da kuma fadi ta shi da yawa tun daga farko har zuwa yau, sun isa wani muhimmin mataki mai muhimmanci. A yau Musulmai na iya taka muhimmiyar rawa ta tarihi. A yau, ranar da hangen nesa na nasarar gaskiya a kan ƙarya, da Musulunci a kan kafirci, ya kusanci zahiri fiye da dukan shekarun da suka gabata.

Sharadi na farko na wannan muhimmin abu, shi ne hadin kan Musulmai. Hadin kan Musulmai a gaban kafirci na duniya, dabara ce ta Alkur'ani da kuma koyarwa ta asali daga Musulunci mai tsafta na Muhammad (SAW), ba wani lamari na sama-sama mai wucewa ba. Ma'anar hadin kai shine, a matakin jama'a na al'ummomin Musulunci, a mayar da batutuwan da suka hada kowa a matsayin tushe da ginshiki. Duk da, ana ƙoƙarin, ta hanyar hujja da kuma kiyaye dukkan abubuwan 'yan'uwantaka da taimakon juna, kamar yadda koyarwar Alkur'ani ta nuna, a cikin cikakken zaman lafiya, ya zamo an mayar da batutuwan da aka bambanta akansu zuwa batutuwa da akai hadakayya akai.

Abin da yake tabbata shi ne, daidaikun Musulmai a al'ummomin Musulunci, idan suna fuskantar kafirci na duniya, su sanya ka'idar Alkur'ani ta "masu tsanani a kan kafirai, masu rahama a tsakaninsu" a matsayin tushen tunani, magana, da aiki, kuma ta haka ne ake samun hadin kan Musulunci. Duk lokacin da kowane ɓangare na wannan sakon sama yayi nesa daga matakin aiki na Musulmai, to za su yi nesa daga wannan matsayin 'yancin kai da suka samu a cikin birnin Musulunci, kuma wannan doka ce da ba a saba ma ta.

Wannan doka tana ɗaya daga cikin ka'idoji da sakwannin juyin juya halin Musulunci. Lokacin gudanar da makon hadin kai na farko ya fara ne daga watan Maris na shekara ta 1978 (watan Isfand na shekara ta 1356 na kalandar Farisa) a lokacin gwagwarmaya da gwamnatin Pahlavi; lokacin da jagora shahidi mai girma (Allah ya daukaka darajarsa) a lokacin gudun hijirarsa a Iranshahr, ya gabatar da wannan tunani, kuma Shi'a da Sunni sukai maraba da shi. Ba da daɗewa ba bayan nasarar juyin juya halin Musulunci, bisa ga Shirin mai kafa jamhuriyar Musulunci, Imam Khomeini (Allah ya tsarkake ruhinsa), "Makon Hadin Kai" ya zama an kafa shi a hukuma. Da yardar Allah, batun hadin kai tsakanin al'ummar Musulunci, yana da nasara a tsakanin al'ummar Iran, kuma makircin makiya bai yi tasiri sosai wajen lalata shi ba.

Amma babu shakka, maƙiya koyaushe suna cikin makirci ga wannan babbar ni'ima. Abin da ke ba su fata shi ne nuna bambance-bambance. Bambance-bambancen akida da addini, duk da yake suna ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da makiya Musulunci ke so kuma suna dogaro da su sosai, amma ba za su tsaya a kan haka ba, za su yi ƙoƙari su mayar da bambance-bambancen kabilanci, al'adu, zamantakewa, tattalin arziki, siyasa, da yanki a matsayin ababen fakewa don haifar da sabani tsakanin Musulmai a Iran da kowace kasa ta Musulunci, don ta hanyar hakan su zauna suna kalli rarrabuwar al'ummar Musulunci da raunana ƙarfinta, kuma a lokacin da ya dace su mamaye su. Umurnin Alkur'ani mai girma a cikin wannan aya mai girma ya bayyana cewa: "Kada ku yi jayayya, don zaku sha kaye kuma ikonku ya bice." Don haka duk mutumin da ya aikata wani abu da zai haifar da rarrabuwa tsakanin Musulmai kuma ya haifar da jayayya a cikin al'ummar Musulunci, ko da sani ko ba sani, da son rai ko ba da son rai ba, yana taimaka wa manufar makiya Musulunci ne. Kuma ta yaya a wannan zamani mutum zai iya danganta irin wannan aiki da jahilci da sakaci, yayin da a yanzu azzaluman duniya, kuma a kan gaba, Amurka mai ta’addanci ta yaye abin rufen fuska na yaudara daga mummuna manufofin mulkin mallaka da makircin 'yan mulkin mallaka da neman mamaya, kuma ta cire safofin hannu masu taushi na yaudara, ta bayyana faratanta masu zubar da jini ga dukan duniya?

Yanzu lokaci ya yi da Musulmai za su yi tunani kuma su kalli abubuwan da suka faru da kyau. Shin idan Musulmai suna da hannu ɗaya da ke dunƙule da ƙarfi, al'ummar Falasdinu za su fuskanci irin wannan zalunci da laifukan mamaya ba tare da kariya ba? Kuma shin idan al'ummai da gwamnatocin da ke gefen Tekun Farisa sun kafa haɗin kai a ƙarƙashin tutar Musulunci, 'yan iska marasa asali da fasikai za su sami ƙarfin zuwa daga dubban kilomita su yi kwadayin ƙasashensu da dukiyoyinsu?

Nasihata da na ke kara jinjinta da maimaita ta a nan a gare ku da nake ba mahukuntan kasashen Musulunci, musamman kasashen yankin yammacin Asiya da gefen Tekun Farisa, shi ne: ku gane makiyinku na gaskiya, ku fahimci makircinsa, ku tunkare shi. Maganin matsalolin al'ummar Musulunci shi ne hadin kai, zumunci, da taimakon juna a kan hanyar alheri da nagarta. Mahukunta masu ta’addanci Amurka da tsarin karya na sahyoniyya su ne makiya na gani kasheni na wannan hadin kai da zumunci. Ba su ba iya makiya jamhuriyar Musulunci da al'ummar Iran da babban fagen gwagwarmayar Musulunci kawai ba ne; a'a, sai dai sun kasance maƙiya ga dukan al'ummar Musulunci, ciki har da al'ummomin yammacin Asiya da arewacin Afirka, kuma a wannan batun, mahukuntan waɗannan kasashe, waɗanda da yawansu ake ɗaukar su a matsayin abokan aikinsu, ba su da 'yanci daga wannan; kamar yadda rashin girmamawa a fili da kuma amfani da kalmomi masu banƙyama ga wasu shugabannin kasashen Musulunci daga shugabannin 'yan mulkin mallaka, yana cikin ƙwaƙwalwar ku da mu.

Muhimmin darasi na hadin kai da rashin jayayya, shi ne darasi na farko na makarantar Musulunci game da yadda ake fuskantar makiya da abokai. Amma darasi na biyu, shi ne kare juna a gaban kafirci, darasi na uku kuma shi ne nau'ikan hadin kai da taimakon juna a fannoni daban-daban na rayuwar Musulmai na kayan duniya da na ruhaniya, dangane da dukiya, tsaro, ilimi, da ci gaba, wanda ƙarshen wannan hanya zai kai ga samun sabuwar wayewa ta Musulunci. Don haka hadin kai tsakanin Musulmai shi ne ginshiki na farko don cimma wayewar Musulunci mai daraja kuma mai nasara. Wannan kunshin na tunani, wanda burinmu ga duniyar Musulunci ke cikinsa, ya sami nasara mai kyau a Iran, kuma nasihar wannan bawa ga al'umma ita ce, kada su bari a sami wani sabani a tsakaninsu.

A karshe ina fata, da ceton Annabi da iyalansa masu tsarki (SAW), inuwar rahama da albarkar Allah ta sauka a kan al'ummomin Musulunci, kuma su ci gaba da bin umarnin Allah, su kara hawan matakan ci gaba da 'yancin kai.

Wassaalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuh

Sayyid Mujtaba Hosseini Khamene'i

8 Ga Shahrivar, 1405

17 Ga Rabi' Al-Awwal, 1448

…………..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha