31 Agusta 2026 - 17:59
Source: ABNA24
Iran Ta Lalata Kayan Aikin Soji Da Wuraren Da Jiragen Yakin Makiya Suke Ajiye + Bidiyo

Rundunar Tsaro ta Juyin Juya Halin Musulunci ta sanar da cewa: An lalatar da kayan aikin fasaha da gyare-gyare da kuma wuraren da jiragen yakin makiya suke ajaiye a sansanonin sojan saman Amurka guda biyu na Malik Hussein da Al-Azraq.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Sojojin ta'addanci na Amurka a yammacin ranar Lahadi, 30 Ogusta 2026, sun sake keta 'yancin kasa da 'yancin kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda suka kai hari a wasu sassan tsibirin Lark, wanda ya haifar da shahada da raunata wasu masu kare ƙasa da 'yan'uwanmu masoya, da kuma barnar dukiyoyin jama'a da fafaren hula.

Rundunar Tsaro ta Juyin Juya Halin Musulunci da sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, a matsayin mayar da martani ga wannan cin zarafin makiya, nan take suka mayar da martani mai tsanani ga makiya Amurka da sahyoniyya ta hanyar tsara wannan aiki.

Rundunar Tsaro ta Juyin Juya Halin Musulunci a cikin wata sanarwa ta bayyana cewa: Ta lalata kayan aikin fasaha da gyare-gyare da kuma wuraren da jiragen yakin makiya suke tsugunna a sansanonin sojan sama na Amurka guda biyu na Malik Hussein da Al-Azraq.