Shugaban kungiyar 'yan uwa musulimin Sheik Ibrahim Alzakzaky ya bayyana wa manema labarai cewa ya rasa 'ya'yan sa guda uku a cikin wannan hari.
Al Zakzaky ya yi zargin cewa sojoji ne suka budewa 'yan uwa musulmi wuta bayan kammala mazahara a ranar jumu'a.
Har yanzu dai jami'an Soji ba su ce komai ba dangane da zargin cewa Sojoji ne suka kaddamar da harin. ABNA