Jirgin na dauke da mutane 116 daga cikinsu 50 'yan kasar Faransa ne.
Kamfanin Air Algerie ya ce sadarwa ta katse da jirgin kimanin minti 50 da tashinsa daga birnin Ouagadougou a Burkina Faso.
A yanzu an soma gudanar da bincike a arewacin Mali tun daga garin Gao zuwa Tessalit.