Limamin juma’ar na Tehran Ayatullah Ahmad Jannaty ya ce kasashen Amurka da Birtaniya da H.K. Isra’ila su ne tushen matsalolin da wannan yankin ya ke fama da shi, wanda shi ne dalilin yin shirun kungiyoyin kasa da kasa akan abinda ya ke faruwa a kasashen Iraki da Palasdinu. Ayatullah Ahmad Jannaty ya yi Allah wadaida da ayyukan ta’addancin da kungiyar takfiriyyah ta ke tafakwa a cikin kasar Iraki sannan ya kara da cewa: “Yan ta’adda suna tafka laifi da sunan Musulunci kuma suna samun cikakken goyon baya daga turai. Ayatullah Jannaty ya kuma yi Allah wadai da kisan da ‘yan sahayoniya su key i wa al’ummar Palasdinu sannan kuma ya jinjjnawa shirun da kungiyoyin kasa da kasa su ke yi akan abinda ya ke faruwa.ABNA
12 Yuli 2014 - 10:41
Lambar labari: 623338
Wanda ja ya jagoranci sallar Juma’a anan Tehran ya yi suka akan shirun da kungiyoyin kasa da kasa su ka yi akan laifukan da h.k. Isra’ila ta ke tafakwa akan al’ummar palasdinu