A hudubar sallar juma'arsa a babban Masallacin juma'ar birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yau; Limamin da ya jagorancin sallar juma'ar Ayatullahi Sayyid Ahmad Khatami ya bayyana cewar halartar taron tunawa da cikan shekaru 25 da rasuwar Imam Khomeini {r.a} yana dauke da sakonni biyu masu muhimmanci; Sakon farko shi ne jaddada mubaya'a ga tafarkin Imam Khomeini da kuma sakon jaddada mubaya'a ga magajinsa Ayatullahi Sayyid Ali Khamene'i jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran.
Har ila yau Ayatullahi Ahmad Khatami ya tabo batun ranar 15 ga watan Khordod wato 5 ga watan Yunin shekara ta 1963, ranar da tsohon sarkin Iran Muhammad Ridha Shah Fahlabi ya zubar da jinin al'ummar kasar, a matsayin farkon yunkurin samar da juyin juya halin Musulunci a Iran, inda jinin al'umma ya zame tamkar takin da ya kara ruruta wutar neman juyi a duk fadin kasar.ABNA